Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul-Baiti (A.S) - ABNA - ya habarta cewa, Duk da matakin da majalisar dokokin yahudawan sahyuniya ta dauka na dage shirin amincewa da shirin sauyin shari'a a majalisar Knesset har zuwa yau litinin, sahyoniyawan suna ci gaba da gudanar da zanga-zangar adawa a yankunan da suka hada da Tel Aviv, Haifa da Ra'anana.
Kafofin yada labaran yahudawan sahyuniya sun bayar da rahoton cewa, kimanin yahudawan sahyoniya dubu 100 ne suka gudanar da zanga-zanga a birnin Tel Aviv domin nuna adawa da shirin sauye-sauyen shari'a na Firaminista Benjamin Netanyahu.